Za’a fara ganin canji daga 2018- Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya jaddada kokarin da gwamnatin su a karkashin mulkin shugaban kasa Buhari take yi don ganin yan Najeriya sun fara ganin canjin da suka zaba a kasa, kamar yadda shi kan sa shugaba Buhari ya bayyana a sakon taya murnar Sallah.

Farfesa Yemi Osinbajo

Farfesa Yemi Osinbajo

Jaridar Premium Times ta ruwaito Osinbajo yana bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da yan jaridu bayan addu’ar ibada daya gudana a wata cocin garin Abekuta, inda yace “gwamnatin mu ta dage wajen tabbatar da kasar nan kan turba mikakkiya.”

Mataimakin shugaban ya kara da cewa sai dai, ba za’a fara cin moriyar canjin ba, har sai nan da shekarar 2018. Yace “mun san jama’a da dama zasu rika tambayar wai ina canjin ne?, jama’a za suyi suka, amma mu kam a shirye muke, kuma muna jajircewa tare da tabbacin cewa Allah na tare damu, don haka ba zamu ji kunya ba.” Ya kara da cewa “nan da wani lokaci zamu fara cin moriyar canji, zamu ga bambamcin” “akwai gudunmuwar da kowa zai bayar, dole ne yan Najeriya su dinga nuna kishin kasa a al’amuranmu”

KU KARANTA:Boko Haram Na Kashe Musulmai Ne Da Christa – Osinbajo

Osinbajo ya lissafa fasa bututun mai da tsagerun Neja Delta keyi a matsayin babban abinda ya jefa kasarnan cikin halin matsin tattalin arziki, yace aikin tsagerun yayi sanadiyyar Najeriya yin asarar kashi 60 na kudaden shiga.

“Daya daga cikin musabbabin da yasa kasar nan ta shiga matsin tattalin arziki shine fasa bututun mai da tsagerun Neja Delta keyi, sanadiyyar haka muka rasa kasha 60 na kudaden shiga, tare da asarar kasha 40 na iskar gas.” Inji Osinbajo.

Sai dai duk da wadannan matsaloli daya zayyanu, Osinbajo na da yakinin tare da tabbacin tattalin arzikin Najeriya zai farfado nan bada dadewa ba. “da zarar mun warware wannan matsalar, zamu fara samun karin kudaden shiga” inji shi.

Source

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *