PDP ta kara sukar Buhari bayan ya gabatar da Sakon Idi

Ka tsaya kayi aikin ka, ka daina ganin laifin mu-PDP tace da Shugaba Buhari

PMB(1)

 

 

 

 

Jam’iyyar adawa ta Kasar nan, ‘The Peoples Democratic Party’ (PDP) ta kira Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da ya nemi hanyar gyara Kasar nan, ba ya tsaya ganin laifin su ba. Jam’iyyar adawa ta PDP tace Kasar tana cikin matsala, musamman yanzu da aka samu durkushewar tattalin arziki. PDP tayi kaca-kaca da Muhammadu Buhari ne jim kadan bayan ya gabatar da sakon sa na Bikin Idi ga ‘Yan Najeriyar.

Dayo Adeyeye, na Jam’iyyar ne ya bada wannan jawabi a jiya. PDP ta zargi Shugaba Buhari da ganin laifin ta cikin game da karayar arzikin da Kasar ta shiga. Shugaba Buhari yace laifin Gwamnatin baya ne da kuma matsalar tattalin arziki na duniya ya jefa Kasar cikin wannan hali. Jam’iyyar ta PDP tace dole Shugaba Buhari ya daina daura nauyi kan kowa, ya tsaya yayi aikin sa. Jam’iyyar adawar ta PDP ta tunatar da Shugaba Buhari yadda Kasar ta magance matsalar tattalin arzikin da duniya ta shiga a shekarar 2010.

KU KARANTA: Bikin Sallah; Masu raguna, ba ciniki!

PDP dai tace dole Shugaba Buhari na Kasar da Jam’iyyar sa ta APC su kawo ‘Canjin’ da suka yi alkawari ga al’umma ba su tsaya kuka ba. Lokaci yayi da Shugaba Buhari za su yi kokarin shawo kan matsolin wannan Kasar da suke jefa mu ciki, Inji PDP. Sai Shugaba Buhari ya cika alkawuran da APC tayi na bogi. PDP dai ta kara da cewa tana taya Musulman Kasar murnar Idi, ta kuma yi kira da su, suyi koyi da baban mu Annabi Ibrahima. Jaridar The Cable ne dai ta rahoto wannan bayani.

Shugaba Buhari dai a sakon idin sa, ya bayyana cewa matsalar tattalin duniya ne da kuma rashin adana ya cuci Najeriya. Don haka ba za a iya raba jiya da yau ba. Ya dai bayyana cewa Gwamnatin san a kokarin magance wannan matsala, ya kuma kira da a hada kai a Kasa.

Source

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *