Labari da dumi-dumi: Tsoro da kuma rudani kamar yadda girgizan kasa ta afku a jihar Kaduna

Wani rahoto yace Kwoi, headkwatar karamar hukumar Jaba dake jihar Kaduna, ta fuskanci girgizan kasa wanda ya haddasa tsoro da rudani, a ranar Lahadi, 11 ga watan Satumba.

Kwoi na a yankin  Kudancin jihar Kaduna.

Kaduna

gwamnan ya tabbatar da cewa wani yanki na jihar sun fuskanci girgizan kasar

An tabbatar da al’amarin a wata sanarwa da sa hannun Samuel Aruwan, kakakin gwamna Nasir el-Rufai, da kuma wanda hukumar NAIJ.com ta samu, cewa gwamnatin jihar ta roko kan mutane suk wantar da hankalinsu.

Gwamnatin tace tayi rahoton al’amarin ga hukumar da ta dace domin ta binciki ci gaban, ta ba da rahoto kan al’amarin da kuma kula da ta dace.

KU KARANTA KUMA: Wole Soyinka ya la’anci hana zanga-zangan BBOG

Sanarwan ta bayyana cewa, gwamnan, Mallam Nasir Ahmed El-Rufai ya tabbatar da cewa an sanar da masana ilimin kasa da hukumomin gaggawa al’amarin.

Sanarwan tace: “Gwamnan ya tausayawa mutane a yankin kwai kan girgizan gasa da aka rahoto ya afku a yankin.

“Ya umarci hukumar ma’aikatar gaggawa (SEMA) da ta duba yankin da kuma samar da kwanciyar hankali gay an kasar.

 “An kuma sanar da hukumar dillancin kasar, an kuma gayyace su domin bincikar girgizan a yankin Kwoi su kuma samar da shiriya da ya dace.

 “Ya umarci hukumar ma’aikatar gaggawa (SEMA) da su binciki yankin da kuma samar da kwanciyar hankali da yan kasar.

Source

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *