Wata yar Najeriya tayi kashin daurin hodar iblis 5

–Ms Binuyo Basari ta baiwa mutane mamaki yayinda tayi kashin daurin hodar iblis 5

–Wannan na faruwa ne bayan mako daya da tayi kashin daurin hidar iblis 75

–Iyabo tayi shirin zuwa aikin hajin bana yayinda Hukumar yaki da mugayen kwayoyi NDLEA sukayi ram da ita

drugs

Wata mata yar shekara 55 mai suna Binuyo Busari ta kara yin kashin daurin hodar iblis guda 6, mako daya bayan tayu kashiin dauri 76 .

Iyabo tayi shirin zuwa aikin hajin bana yayinda Hukumar yaki da mugayen kwayoyi NDLEA sukayi ram da ita a lokacin da suke binciken mahajjata a jirgin da ke tafiya daga Abuja zuwa Madina.

A wata jawabi da kwamandan NDLEA, Hamisu Lawan, ya saki jiya a babban filin jirgin saman Abuja, yace za’a hukunta matan bisa ga dokan kasa.

Lawan ya bayyana cewa jimillan daurin hodar iblis din da tayi kashi 82 ne.

KU KARANTA:Hukumar kasar Saudiyya na gargadi ga mahajjata

Ya ce: ”Ms Binuyo Basari ta yi kashin daurin hodar iblis 82 mai nauyin gram 931. An shirya komai domin gurfanar da ita.

Iyabo ta bayyana abinda ya faru : “Wanda ya dauki nauyi na yace zai biya mini kujeran haji. A haka na fara shuga galin. Ina son harkan har sai lokacin da aka fara aikin muguyan kwayoyi. Na so inki amma ina. Banda haka ma, anyi mini alkawarin naira miliyan 1 kuma na yarda. Na hadiye daurin hodar a legas kuma na dau jirgin legas zuwa Abuja amma a hanyan zuwa madina aka kamani.

Source

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *