Ta auri dan Sandan da ya ceci rayuwar ta a Maiduguri

– Blessing Asso ta gidan Talabijin nan na Channels TV ta auri wani dan Sanda

– Emmanuel Asso ne dan Sandan da ya ceci rayuwar ta lokacin da ‘Yan Boko Haram suka tada wani bam a Maiduguri

– Tun daga nan kuma suka shaku, ga shi har sun yi aure kwanan nan

vllkyt6rt3rgbtp1p.93305388

vllkyt738m8hg6eee.87767adf

 

 

 

 

 

 

Abu karamar wasa… karamar magana ta zama babba!

Ango Emmanuel Asso da Amaryar sa Blessing Asso ranar daurin auren su!

Fitacciyar ‘Yar Jaridar nan ta gidan Talabijin Channels TV ta auri wani dan sanda mai suna Emmanuel Asso. Blessing da Emmanuel sun hadu ne dai asali lokacin da ‘Yan Boko Haram suka harba wani bam a Garin Maiduguri na Jihar Borno. Blessing tana aikin ta ne game da Kungiyar Boko Haram a Maiduguri a wancan lokaci, kwatsam sai bam ya tashi a inda ta ke daukar hoto, a wannan lokaci ne wannan dan sanda ya taimake ta.

KU KARANTA: Boko Haram sun sace mata 3000 a Maiduguri

Emmanuel Asso, Jami’in dan sanda ne, ya kuma ceci rayuwar Blessing daga wannan hari. Amaryar ta sa ta bayyana cewa shi ya taimake su, ya ajiye su a gidan sa, su ka kwana, bayan an tarwatsa inda ta ke aiki. Wannan abu ya faru ne a Maidguri, tun daga nan fa suka kulla zumunci, ga shi yanzu sun zama mata da miji.

KU KARANTA: Boko Haram sun sace mata 3000 a Maiduguri

Wannan labari ya kayatar da kowa kwarai da gaske. Muna addua Ubangiji ya ba su zama lafiya!!

Source

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *