Marainiya ta ciri tuta a Kasar Sudan

Marainiya ta ciri tuta a Kasar Sudan

Sudan student

 

 

 

Wata Marainiya ‘Yar Kasar Najeriya mai suna Islamiyat Oluwatoyin Abdulkadir ta ciri tuta a Kasar Sudan inda tayi karatu. Oluwatoyin Abdulkadir ta zo ta daya a cikin sa’annin ta da suka karanta ilmin likitanci a Babban Jami’ar Afrika ta Kasar da ke Khartoum, a Kasar ta Sudan. Oluwatoyin Abdulkadir ta rasa iyayen ta ne tun tana shekara 6 a duniya ta shiga cikin littafin Tarihi. Oluwatoyin Abdulkadir Islamiyat tace ita kan ta wannan abu ya bata mamaki.

Abdulkadir tana fadawa Kafar watsa labarai ta NAN ta wayar tarho yadda ta taki irin wannan sa’a. Oluwatoyin ta rasa mahaifiyar ta tun tana ‘yar shekara 3 da haihuwa, bayan shekaru 3 kuma, uban ta ma ya rasu. Ta dai zama cikakkiyar marainiya tun tana shekara 6 a duniya, Oluwatoyin Abdulkadir tace ta taki kafar dama a rayuwa, musammman zuwan ta Kasar Sudan. Oluwatoyin tace ita har yanzu nasarar da ta samu a rayuwar karatu yana ba ta mamaki matuka, ba ma karatun ba kadai, gaba daya abin da ya shafi rayuwar ta, tana ganin sa kamar mafarki ko wani siddabaru! Oluwatoyin ta bayyana yadda wata baiwar Allah mai suna Alhaja Sekinat Adekoka ta taimake ta a rayuwa bayan ta rasa kowa.

READ ALSO: Babu ruwan mu da Kungiyar BBOG-Matan Kirista

Oluwatoyin Abdulkadir tace bayan da ta rasa Mahaifan ta, kakar ta ta cire ta daga makaranta, sai mai makarantar da kan ta, Alhaja Sekinat Adekola, ta dauki nauyin karatun firamaren ta har sakandare. Wannan ta’alika ta dauki har nauyin jarabawar ta ta shiga Jami’a. Bayan ta rubuta jarabawar JAMB ta kuma samu maki 274, dama can burin ta ita ta zama likita, sai dai saboda rashin wadata, ta hakura da karantar likitancin.

Kwatsam kuma sai Ubangiji ya taimake ta ta samu kyautar zuwa karatu a babbar Jami’ar Afrika ta Kasar da ke Khartoum ta Sudan. Har ga shi yau ta kammala karatu da makikin da ba a taba samun irin sa ba a Jami’ar.

 

Source

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *