Gwamnatin Jihar Sokoto za ta raba naman Sallah ga marayu

– Gwamnatin Jihar Sokoto za ta raba nama har na Naira miliyan 11 ga Marayu domin hidimar Sallah

– Za a raba shanu a kowace Karamar Hukuma daga cikin kananan Hukumomin Jihar gida 23

– Za ta yanka sa guda daya ga marayu 50, akwai dai marayu kusan 4,205

Aminu-Tambuwal

 

 

 

Gwamnatin Jihar Sokoto za ta raba nama domin Bikin Babbar Sallah ga marayu. Hukumar Dillancin labarai na Kasar watau NAN ta ba da wannan rahoto. Gwamnatin Jihar ta Aminu Waziri Tambuwal za ta kashe Naira Miliyan 11 wajen sayen shanu ga marayu 4,205 da ke Jihar. Shugaban Kwamitin Zakka na Jihar, Alhaji Lawal Maidoki ya bayyana hakan.

Alhaji Lawal Maidoki ya bayyana cewa an ba kowace gunduma na fadin Kananan Hukumomin Jihar kudi Naira 130,000 domin sayen shanu. Kowace gunduma za ta samu sa guda daya da za ta raba domin marayu 50. Za ayi wannan abu ne domin taimakawa Marayu a Jihar. Alhaji Maidoki yace an bi matakan tabbatar da cewa kudin ba za su salwanta ba.

KU KARANTA: Gwamna Ambode zai dauki mataki ga masu lalata da kananan yara

Shugaban kwamitin Zakkar ya tabbatar da cewa za a sa ido wajen ganin an raba wannan nama daidai wadaida. Ya kuma yi kira ga lawanai su dage wajen ganin an yi abin ya dace wajen ganin kowa da kowa ya samu wannan nama.

Gwamnatin Tarayya dai ta sanar da cewa za ba da hutun Bikin Idin ne a Ranar 12 da 13 ga watan Satumban nan. Ministan al’umurran cikin gida, Lt. Gen Abdulrahman Dambazau (rtd), ya bada wannan sanarwar ta bakin Sakataren Ma’aikatar Muhammadu Maccido.

Source

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *