FG ta kashe N5bn akan jiragen shugaban kasa a watanni 15

–Gwamnatin tarayya ta kashe N5bn akan jirage 10 na shugaban kasa tun watan Mayun 2015

–An kashe N2.3billion tsakanin watan Mayu da Nuwamban 2015

–Fadar shugaban kasa ta ce ta kashe N1.350billion Domin biyan bashin da ake bi tun 2014

Buhari air fleet

Gwamnatin tarayya ta kashe kudi N5bn akan jirage 10 na shugaban kasa tun watan mayun 2015 da ta dau ragamar mulki ,game da wata takarda da Jaridar punch ta samu.

Jerin filla -filla yadda aka kashe kudin ya nuna cewa ofishin babban akawun tarayya ya saki N2.3billion ga PAF tsakanin watan mayu fa nuwamban 2015.

Game da cewar takardan, kudin N2.3billion ya kunshi kudin kai,manyan ayyuka ,cikin kudi 5.19 billion da aka sanya ma PAF a kasafin kudin 2015

Daga cikin N2.3billion, fadar shugaban kasa ta ce an kashe N99.715millionwajen kula da jiragen ,siyan spiya da kuma sabis,yayinda kashe N98.5million wajen ayyuka.

KU KARANTA:Buhari ze rage yawan jiragen hawan shugaban kasa-Garba Shehu

An kashe N165.373million wajen hori, kuma an kashe N85.5million akan kiwon lafiya da overheads. Kana Fadar shugaban kasa ta ce ta kashe N1.350billion Domin biyan bashin da ake bi tun 2014. Kuma an mayat da N500million ga ofishin NSA da aka ci bashi kafin a saki kudi.

Amma game da cewar masana jiragen sama, gwamnatin tarayya ta kashe N19.9billion sabanin kudin da tace ta kashe akan jirage 10. Masanan sunyi lissafinsu ne akan kudin kula da jiragen ne wanda kimanin$65.13million idan aka juya najeriya kuma 19.9 billion.

Source

You may also like...

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *